Constitution of the Federal Republic of Nigeria

Chapter IV: Fundamental Rights
#Law2Go version: HAUSA

SASHI 33: Yancin rayuwa da rai (kai ka ke da ranka)

 • Kai da sauran da duk sauran ‘yan adam a duniya na da yancin rayuwa da rai. Doka ta hana kisan mutum.

SASHI 34: Kowa na da yancin rayuwa da girma da martaba (ka na yancin rayuwa da martaba domin kai ba bawan kowa ba ne)

 • Dole ka dauki duk dan adam da martaba da girma ko kana kaunar sa ko baka yi. Kai ma ka dace a dauke ka da martaba da girma.

SASHI 35: Yancin Rayuwa da sakewa: ba matsi ko fitina (Ka na da yancin sakewa a rayuwar ka)

 • Ka na daman rayuwa da sakewa: banda matsi ko fitina.
 • Amma doka ta bada izini ga hukuma ta hana ka sake wa idan:
  • Kotu ta ba da izini a kama ka ko a rufe ka domin  ka karya doka, ko ka ki yin biyaya akan hukuncin ta;
  • Ko kai yaro ne wanda yake kasa da shekara sha takwas;
  • Ko idan ka nada cuta da ke saurin yaduwa kaman ciwon ebola;
  • Ko idan ka haukace;
  • Ko idan ka saba da shan kwayoyi da giya.
 • Ko ana zaton ka yi karya doka ne kuma a na kan yin maka sharia, doka bata ba da izini a kama ka a rufe na tsawon lokacin da ya fi lokacin da za a rufe ka idan kotu ta same ka da laifi ba. (A misali, hukuncin laifin satar shanu a karkashin doka, shekara biyu ne. saboda haka, idan an kule mutum na lokacin da ya kai shekara biyu, kotu za ta sake shi ba bata lokaci).
 • Idan aka kama ka ko aka rufe ka, ka na damar yin shuru ka ki yin Magana sai ka tuntubi lawyan ka. Doka ta hana yan sanda da sauran jami’an tsaro su tilasta ka ka yi kamin ka tuntubi lawyan ka.
 • Idan yan sanda ko sauran jami’an tsaro su ka kama ka , dole ne su fada maka a cikin kwana daya, a rubuce da yaren da ka sani, dalili da su ka kama ka da rufe ka.
 • Idan hukunchi da ya biyo laifin karya doka ba kasha mai laifin bane, bai dace a kamo mutum ko a rufe na lokaci fiye da kwana daya ba, bada an kai sa kotu ba sai dai idan babu kotu a kilomita arba’in daga inda a ka rufe shi. Idan ya kasance haka, sai a kai sa kotun a cikin kwana biyu ko cikin lokaci.
 • Idan a kama ka ko rufe ka ba da laifi ba, kana da ‘yancin a biya ka, da kuma nemi gafaran ka daga gun hukuma.

SASHI 36: ‘Yanci a saurare ka a kotu (Ka na da daman a ji ra’ayin ka kafin a yanke sharia)

  • Ka na da daman a saurare ka a cikin sharia.
  • Kai ba mai laifin karya doka bane sai shari’a ta yanke hukunci.
  • Idan wani na zaton ka karya doka, shi ke da nauyin nuna ka yi laifi ba wai kai ka nuna kayi laifi ba. (Sai dai idan doka ta saka ka ka nuna baka yi laifin ba).
  • Idan an kai ka gaban kotu domin ana zaton ka yi laifin karya doka, ka na da ‘yanci a gaya maka cikin lokaci da yaren da ka sani, irin laifin da ake zaton ka yi. Kuma ka na da ‘yancin a baka lokaci da dama da zarafin Karen kanka a kotun ko da kan ka ko ta lawyan ka.
  • Ka na da ‘yancin tambayan shedun wanda su ka kawo karan ka kuma ka na da ‘yancin kiran shedun ka.
  • Idan baka gane yaren da ake yin amfani da shi a kotun ba, ka na da ‘yancin yin amfani da masu fassara kyauta.  
  • Idan shari’a ta yanke hukunci, ko kai ko iyalin ka na da ‘yancin karban takardun yanke hukunci cikin kwana bakwai.
  • Ba za a same ka da laifin karya doka ba idan abunda kayi doka ba ta hana ba a lokacin da kayi shi. (A misali, doka ba ta hana yin kiwo a waje a shekaran dubu biyu da sha biyar, amma ta hana yanzu a jihohi da dama ba. Sab da haka, ba za a iya kama mutum da laifin yin kiwo a waje a shekarun da su ka wuce.
 • Ba za a baka hukunci laifin karya doka da yafi hukuncin da doka ta tsara a lokacin da aka aika ta laifin. (A misali, idan laifin satan mutum a shekarun dubu biyu da sha uku shine kulle mutum na shekara shida, bai dace idan an yanke hukuncin sa ba a wannan shekarun dubu biyu da sha bakwai a bashi rayuwan kurkuku har mutuwa ba. Lokacin da za a yi amfani da shi lokacin da ya aikata laifin ne ba lokacin da a ka yanke sharia ba.
 • Bai dache a yi maka sharia so biyu akan zaton laifin karya doka daya. Doka ta haramta haka. Kuma idan gwanati ta gafata wa mutum laifin sa, ba za a sake yin masa sharia ba.
 • Idan an kaika gaban kotun domin ana zaton kayi laifi karya doka, bas za a saka shi a dole ya bayar da sheda ba.
 • Ba za a daure mutum domin laifin karya doka ba, sai dai idan laifin na rubuche a chikin dokokin kassa. Kuma, laifi irin na gargaja ba laifi bane a dokokin kassa..

SASHI 37: ‘YANCIN RAYUWA CIKIN RUFIN ASIRI DA IYALAN KA (Ka na da ‘yancin rayuwa cikin rufin asiri)

 • Ka na da ‘yanci yin rayuwa cikin rufin asiri da ya shafi gidan ka, na’urar wayar ka da sakuna na kar ta kwana. Doka ta tabatar da kiyaye wannan.

SASHI 38: ‘YANCIN TUNANI, SHA’ANI DA ADDINI (Ka na da ‘yancin tafiyar da rayuwar ka yanda ka so)

 • Ka na da ‘yancin yin duk irin tunani da ka so.
 • Ka na da ‘yancin bin addinin da ka so, ko kai kadai ko tare da jama’a. Kuma doka ta yarda ka canja addinin ka idan ka so yin haka. Babu wanda ya isa ya sa ka ka canja addinin ka idan ba ka son yin haka. Kuma ba dole ba ne ka bi wani addini idan ba ka so. Doka kuma ta haramta zama dan kungiyan asiri.

SASHI 39: ‘YANCIN FADIN ALBARKACIN BAKIN KA DA YADA LABARAI (Kana da ‘yancin fadin albarkacin bakin ka)

 • Ka na da ‘yancin ra’ayinka.
 • Ka na da ‘yancin fadin albarkacin bakin ka.
 • Ka na da ‘yancin fadin ra’ayin ka da kuma yada wannan ra’ayi ga sauran jama’a ba tare da shakkar kowa ba.
 • Idan kana da izinin gwamnati, za ka iya bude gidan yada labarai kaman gidan telebijin, Radio, jaridu da qasidu.
 • Ka na da ‘yancin amfani da bude shafin zumunta na zamani kamar su facebook, twitter, Whatsapp, da dai sauran su.
 • Ba a takura wannan ‘yanci ba idan doka ta hana ka yada  wani bayani da ka samu ta rufin asiri ta hanyar aikin ka a matsayin ma’aikacin gwanati, lawya, likita ko in shari’a ta hana.

SASHI 40: ‘YANCIN TARO KO HULDA DA KUNGIYOYI (kana da ‘yancin hulda da jama’ar da ka so)

 • Ka na da ‘yancin hulda da jama’a.
 • Ka na da ‘yancin bude kungiya ko ka shiga kungiyar kwadago da za ta kare ka. Ka na kuma da ‘yancin ka ki shiga wata kungiya ko ka bar kungiyar alokacin da ka ga dama.
 • Ka na da ‘yancin bude jam’iyyar siyasa ko ka shiga jamiyar da ka so muddin jamiyar nan na da regista a wajen hukumar yin zabe da ake kira INEC.

SASHI 41: ‘YANCIN YIN YAWO DA TAFIYA A DUK BANGARAN KASA (Ka na da ‘yancin yawo yanda ka ke so)

 • Ko wane dan Nijeria na da ‘yancin yawo da zuwa duk bangaren kasar Nijeriya da ya so.
 • Ko wane dan Nijeria na da ‘yancin yin tafiya da kuma  zama a duk bangaren Nijeria da ya so. Ko a kudu, yamma, ko arewa.
 • Idan kai dan Nijeria ne, ba wanda ya isa ya kore ka ko hana ka fita daga cikin kasar Nijeria; ko hana ka shigan kasar Nijeria. Sai dai, idan ka yi laifi a cikin Nijeria ka na neman ka gudu; ko idan Nijeria ta na da shiri da wata kasa cewa idan mutum yayi laifi ba zai iya zuwa ya boye a kasar Nijeriya ba. A nan kam, doka ta ba ma Nijeriya izinin kama mutum ta mika shi domin a yi masa hukunci.

SASHI 42: ‘YANCIN RAYUWA BA BANBANCI KO TSANGWAMA (Ka na da ‘yancin da ko wane dan adam ya ke da shi)

 • Ba dan adam da ke da ‘yancin nuna maka banbanci ko tsangwama domin garin ka, kabilar ka, ko kai na miji ne ko mace, addinin ka, jam’iyyar siyasar ka, ko don yanayin haifuwar ka.

SASHI 43:  ‘YANCIN SAYEN FILI A KO WANE BANGAREN NIJERIYA. (Ka na da ‘yancin saye da zama a gida a duk bangaren Nijeriya da ka so)

 • Ko wane dan Nijeria na da ‘yancin saye da zama a gida ko fili a duk bangaren Nijeriya da ya so. Idan kai dan Arewa ne, ka na iya sayen gida a garin Onitsha. Ko yar kudu ta na iya sayan shaguna a garin Lagos. Ko mutumin da ya fito yamma na iya sayan gida a garin Jigawa.

SASHI 44: KWACE FILIN MUTUM (Ka na da ‘yancin a biya ka diyya idan gwamnati ta kwace filin ka)

 • Idan ya zama dole wa gwamnati ta kwace filin ka, wajibi ne ga gwamnatin ta biya ka diyar wannan fili cikin lokaci. Kuma ka na da ‘yancin shigar da kara a kotu idan baka yarda da yawan kudin da a ka biya ka ba.
 • Duka ma’adanen da ke karkashin kasa ko ruwa, kaman zinari, duwatsu masu tsada da man fetur, mallakar gwamnatin tarayya ne.

SASHI 45: HANI KO TAKURA MUHIMMAN ‘YANCIN DAN ADAM (Gwamnati za ta iya hana ko takura ‘yancin mutum cikin wasu yanayi na mussaman)

 • ‘Yancin rufin asiri da rayuwar iyali (SASHI 37); ‘yancin rayuwa da tunani, sha’ani da addini (SASHI 38) ‘yancin fadan albarkacin bakin ka da yada labarai (SASHI 39); ‘yancin taron hadin kai da hulda da kungiyoyi cikin lumana (SASHI 40); ‘yancin yin yawo da tafiya a duk bangaren kasa (41); na iya raguwa idan doka ta zartas da haka domin tsare jama’a gabadaya, ko tsare lafiyar su da tsaron ‘yancin sauran jama’a.
 • Idan akwai rashin zaman lafiya ko tashin hankali kamar yaki, ‘yancin rayuwa da sakewa na iya raguwa idan majalissar dokokin kasa su ka yarda sannan kuma, Gwamnati ba za ta iya karya dokar da ta hana daure mutum domin laifin da ba ya rubuce ba.

SASHI 46: IZININ KOTU MUSSAMAN DA SHIRIN TAIMAKA WA TALAKAWA WAJEN SHARI’A (Kana da ‘yancin a yi ma adalci)

 • Idan ka  lura cewa ana neman takura ma ko hana ka daya daga cikin ‘yancin da su ke SASHI 33 zuwa 46 da ke cikin kundun tsarin mulkin Nijeriya, kana da ‘yancin ka je babban kotun jihar ka gurfana kara.
 • Majalissar dokoki na kasa za su tanada taimakon kudi, do na ba wa wanda bai da karfin daukar lawya.
Do NOT follow this link or you will be banned from the site!